Home Labaru Apc Ta Nesanta Kan Ta Da Ziyarar Da Tinubu Zai Kai Wa...

Apc Ta Nesanta Kan Ta Da Ziyarar Da Tinubu Zai Kai Wa Gwamna Wike A Ribas

57
0

Jam’iyyar APC Reshen Jihar Ribas, ta nesanta kan ta daga
ziyarar buɗe manyan ayyukan raya jihar da Gwamna Nyesom
Wike ya gayyaci Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed
Tinubu.

Tinubu dai ya amsa gayyatar ziyarar kwanaki biyu a jihar Rivers, domin ya ƙaddamar da gadar sama da gine-ginen kotun da Gwamna Nyesom Wike ya yi.

Tuni dai gwamna Wike ya bayyana Larabar nan a matsayin ranar hutu, sannan ya yi kira ga jama’a su fito a yi tururuwar tarbar Bola Ahmed Tinubu

A cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na jam’iyyar APC a Jihar Rivers Darlington Nwauju ya fitar, ya ce babu ruwan su da ziyarar da Tinubu zai kai jihar.

Darlington Nwauju, su na ƙalubalantar gwamna Wike ya daina yi mana shisshigin kitsa ma su siyasar raba kawuna, domin babu abin da ya ke yi a jihar Rivers sai raba kawunan ‘yan jam’iyyar APC.

Leave a Reply