Home Labaru Tinubu Ya Ce Gwamnan PDP Wike Ne Ya Taimake Shi Ya Ci...

Tinubu Ya Ce Gwamnan PDP Wike Ne Ya Taimake Shi Ya Ci Zaben 2023

66
0

Zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya ce ba don
goyon bayan da ya samu daga gwamna Nyesom Wike na
Rivers ba, da bai samu nasarar cin zaben shugaban kasa ba.

A ranar 1 ga watan Maris ne, aka bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shekara ta 2023, inda ya samu kuri’u miliyan 8 da dubu 794 da726, yayin da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya zo na biyu da kuri’u miliyan 6 da dubu 984 da 520, sai kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour ya zo na uku da kuri’u miliyan 6 da dubu 101 da 533.

Peter Obi da Atiku Abubakar dai sun fusata da sakamakon zabe, inda su ka dunguma zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon da hukumar zabe ta fitar.

A yayin ziyarar da ya kai jihar Rivers, Tinubu ya bi gwamna Wike zuwa kaddamar da aikin gadar sama ta Raumuokwuta da Rumuola da aka gina a birnin Fatakwal.

Leave a Reply