An sanya dokar takaita zirga-zirga a garin Birnin Gwari da ke
Jihar Kaduna bayan ’yan bindiga sun yi wa garin kawanya.
Daya daga cikin dattawan garin kuma Danmasanin Birnin Gwari, Zubairu Abdulrauf, ya shaida wa Aminiya cewa, bayan harin ’yan bindiga a tsakiyar garin ne shugaban karamar hukumar, Abdullahi Ibrahim Amir, ya ba da umarnin takaita zirgi-zirgga a cikin garin.
Sanarwar da kakakin shugaban karamar hukumar, Mustapha Idris Abdulra’uf, ya fitar ta ce an hana fita da keke ko babur a daukacin garin Birnin Gwari daga 8:30pm na daren 26 ga watan Mayu, 2023.
Ya ce an hana zirga-zirgar mota daga karfe 9:30pm sannan an hana zirga-zirga na kafa daga karfe 10:pm dare, Don haka duk wanda jami’an tsaro suka kama da karya daya daga cikin dokokin nan to ya kuka da kan sa.
Mustapha Idris Abdulra’uf, ya kuma shaida wa mazauna garin cewa an dauki matakin ne saboda kare rayuka da dukiyoyin mutane, ba don a matsa masu ba.














































