Home Labaru Wadata: Remi Tinubu Ta Ce Basu Bukatar Dukiyar Najeriya Domin Su Rayu

Wadata: Remi Tinubu Ta Ce Basu Bukatar Dukiyar Najeriya Domin Su Rayu

280
0

Uwargidan sabon zababben shugaban Najeriya Oluremi Tinubu,
ta ce ita da iyalan ta basu bukatar dukiyar da Najeriya ta mallaka
domin rayuwa, saboda wadatar da suke da ita.

Yayin da take jawabi a wajen addu’oin da aka gudanar domin zuwar sabuwar gwamnati a mujami’ar Abuja, Remi Tinubu ta ce Allah ya wadata su da abinda suke bukata kuma suna masu gode masa, saboda haka basa tunanin yin amfani da shugabancin Najeriya domin azur ta kan su da kudaden talakawa.

Uwargidan sabon shugaban shugaban kasan ta ce itace zata zama matar shugaban kasa mafi yawan shekaru da zata shiga fadar shugaban kasa, ganin shekarun ta sun kai 63, yayin da mai gidan ta ke da shekara 71.

Remi Tinubu tace suna bukatar taimakon Ubangiji domin hada kan jama’ar Najeriya da zimmar samarwar kasa ci gaban da take bukata domin ci gaba da jagorancin nahiyar Afirka.

Uwargidan shugaban kasa mai jiran gado tace kowanne dan Najeriya yana da hakki akan dukiyar da kasar ta mallaka, kuma za suyi iya bakin kokarin su wajen ganin anyi adalci ga kowanne ‘dan kasa domin dawo da Najeriya akan turba mai kyau. Ta bukaci addu’oin ‘yan Najeriya domin sauke nauyin shugabancin da aka dora musu.

Leave a Reply