Tsohon gwamnan jihar Abia kuma zababben dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Abia ta arewa Dr. Orji Uzor Kalu, ya yi alkawarin sasanta Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Bola Ahmed Tinubu.
Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, Kalu ya yi alkawarin shiga tsakanin mutanen biyu, inda ya ce kada a bari siyasa ta haddasa rashin aminci a tsakanin ‘yan’uwa da abokan arziki.
Uzor Kalu, ya roki shugabannin biyu da su maida wukaken su Kube domin dorewar damokradiyyar Nijeriya.
Da ya ke jinjina wa gudunmawar da Saraki da Tinubu su ka bada wajen ci-gaban siyasar Nijeriya, Kalu ya tuna daddadar alakar da ke tsakanin tsoffin gwamnonin biyu.
Ya kuma shawarci kafafen yada labarai su yi taka-tsan-tsan da nuna kwarewa wajen kawo rahoton muhimman batutuwan da su ka shafi kasa.
A karshe ya roki Saraki da Tinubu su rungumi zaman lafiya, ya na mai cewa ba zai saduda ba har sai ya dawo da kyakyawar alakar da ke tsakanin su.
You must log in to post a comment.