Dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya ce jam’iyyar APC ba ta koyi darasi daga abin da ya faru a shekara ta 2015 ba, wanda ya sa Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara su ka zama Shugabannin majalisun dokoki na tarayya.
Yayin da ya ke jawabi a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Shehu Sani ya ce ra’ayin sauran ‘yan majalisar APC a shugabancin majalisar dokoki na iya haifar da maimaicin abin da ya faru shekaru hudu da su ka gabata.
Furucin Sanatan dai ya na zuwa ne, wata daya bayan Shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomole ya ce jam’iyyar ba za ta bari ‘yan majalisar jam’iyyar PDP su jagoranci kowane kwamiti na majalisar ba.
Da ya ke maida martini a kan furucin Oshiomhole, Shehu Sani ya ce kafin a zabi mutum a matsayin Shugaban majalisar dattawa, gasa ce da ke bukatar wani adadin na mutane.
Ya ce matukar ana son dan takarar da jam’iyyar APC ta fi so ya yi nasara, ya zama dole a nemi ‘yan majalisa na jam’iyyar adawa sannan a shiga yarjejeniya da su.
You must log in to post a comment.