Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Jami’an Hukumar Bada Agajin...

Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Jami’an Hukumar Bada Agajin Gaugawa 4

278
0

Wasu gungun ‘yan bindiga, sun bude wuta a kan wasu jami’an hukumar bada agajin gaugawa, inda su ka yi awon gaba da mutane hudu daga cikin su da nufin karbar kudin fansa daga wajen iyalan su kafin su sake su.

Lamari dai ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata, a karamar hukumar Abua-Odual, kamar yadda shugaban hukumar na yankin kudu maso kudu Walson Branden ya tabbatar a garin Fatakwal.

Mista Walson, ya ce ‘yan bindigar sun kai wa ma’aikatan farmaki ne yayin da su ke kididdigar manoman da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar, da nufin ba su tallafin da ya dace domin su cigaba da sana’ar su.

Ya ce a daidai lokacin ne ‘yan bindigar su ka bayyana, inda su ka bude masu wuta har su ka samu daya daga cikin ma’aikatan da harsashi a kafar sa, amma duk da haka sai da ya samu ya tsallake rijiya da baya, yayin da su ka yi awon gaba da sauran ma’aikata hudu daga cikin su har da wata Mace.

Wani shaida da ya gane wa idon sa, ya ce rashin kyawon motar da ma’aikatan ke ciki ne ya sa ‘yan bindigar su ka samu nasarar yin garkuwa da su cikin sauki.

Leave a Reply