Home Labaru Takaddama: ‘Yan Sanda Na Cigaba Da Kalubalantar Sojoji A Kan Kisan Jami’an...

Takaddama: ‘Yan Sanda Na Cigaba Da Kalubalantar Sojoji A Kan Kisan Jami’an Su 3

295
0

Hukumar ‘yan Sandan Nijeriya, ta maida wa sojoji kakkausan martani, bayan hukumar tsaro ta rundunar sojin ta ce jami’an ta sun harbe ‘yan sanda uku ne bisa zargin cewa masu garkuwa da mutane ne.

Sojojin dai sun harbe ‘yan sandan ne, bayan sun kamo wani rikakken dan fashi kuma mai garkuwa da mutane, yayin da su ke kan hanyar zuwa Jalingo da shi.

‘Yan sanda sun zargi sojoji da cewa, da gangan su ka harbe jami’an su, domin bayan sun kashe su sai kuma su ka saki wanda aka kamo ya tsere.

 ‘Yan sandan dai su na daga cikin wadanda su ka ceto Magajin Garin Daura a hannun masu garkuwa da mutane a dajin Kano, sannan su na daga cikin wadanda su ka kamo wasu gaggan shugabannin kungiyar Boko Haram.

Jami’an ‘yan sandan da aka kashe

Jami’an ‘yan sandan da aka kashe kuwa sun hada da Sufeta Mark Ediale dan asalin jihar Edo, da Sajen Usman Dan’azumi da Sajen Dahiru Musa, dukkan su ‘yan asalin Jihar Taraba.