Home Labaru Labarun Ketare India Ta Zargi Pakistan Da Haddasa Ayyukan Ta’addanci A Kashmir

India Ta Zargi Pakistan Da Haddasa Ayyukan Ta’addanci A Kashmir

421
0
Narendra Modi, Fira-ministan India
Narendra Modi, Fira-ministan India

Fira-ministan India Narendra Modi, ya ce matakin kwace kwarya-kwaryar ‘yancin cin gashin kan yankin Kashmir mai rinjayen musulmi na da nufin ceto yankin daga barazanar Pakistan ta fadada ayyukan ta’addanci.

Karanta Wannan: USAID Ta Ware Dala Milyan 300 Domin Inganta Cinikayyar Amfanin Gona

Cikin jawaban da ya gabatar, wanda shi ne karon farko tun bayan daukar matakin kwace kwarya-kwaryan ‘yancin na Kashmir, Firaministan India, Narendra Modi ya ce matakin na da nufin ceto yankin ba wai muzanta masa ba.

A cewar Modi wanda ke jawabi dai-dai lokacin da India ta girke tarin jami’an tsaro a yankin na Kashmir, na da yakinin sabon matakin zai taimaka matuka wajen ceto al’ummar Kashmir daga barazanar tsaro daga Pakistan.

Fira-ministan na India, ya yi zargin cewa Pakistan na amfani da yankin na Kashmir wajen kaddamar da ayyukan ta’addanci a India, wanda kuma ya ce bayan wannan matakin, ya yi imanin cewa Kashmir za ta mike tsaye wajen fatattakar ayyukan ta’addanci.

Cikin jawaba na Narendra Modi dake zuwa dai dai lokacin da Firaministan Pakistan Imran Khan ke cewa baya da shirin amfani da karfin Soji a yankin na Kashmir bayan matakin India na girke tarin jami’an tsaro, Modi ya bayyana matakin da babbar nasara kan abokiyar gabarsu Pakistan.