Home Labaru Takaddama: Tsohon Kakakin Kungiyar Boko Haram Ya Maka Hukumar DSS Kotu

Takaddama: Tsohon Kakakin Kungiyar Boko Haram Ya Maka Hukumar DSS Kotu

269
0

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja, ta tsaida 24 ga watan Mayu, a matsayin ranar da za ta saurari karar neman biyan diyya da tsohon Kakakin Yada Labarai na kungiyar Boko Haram Ali Konduga ya shigar akn Hukumar Tsaro ta SSS.

Ali Konduga, wanda tsohon sakataren yada labarai ne na kungiyar Boko Haram kafin a kama shi, ya shigar da kara ya na neman diyyar naira dubu 500,000 daga hukumar tsaro ta SSS, saboda sun tsare shi tsawon karin wasu shekaru uku bayan cikar wa’adin da aka yanke masa hukunci.

Lauyan Konduga Mohammed Tola ya shigar da karar a madadin Konduga, inda ya maka Babban Daraktan hukumar tsaro ta SSS da Atoni Janar kuma Ministan Shari’a kotu.

Tola ya bayyana wa kotun cewa, an tauye ma wanda ya ke karewa hakkin sa a matsayin sa na dan Adam kafin a sake shi cikin shekara ta 2016.

Leave a Reply