Babban mai taimaka wa gwamnan jihar Sokoto a kan ayyukan musamma Yusuf Dingyadi, ya bukaci mutanen jihar su kauda bambance-bambance ra’ayin siyasa, a rika yi wa gwamnatin Tambuwal addu’o’in samun nasarar aiwatar da ayyukan ci-gaban jihar Sokoto.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a Sokoto, Dingyadi ya bukaci al’ummomin jihar Sokokto su zauna lafiya da juna ba tare da nuna bambancin siyasa ba, ya na mai bada tabbacin cewa mulkin Tambuwal na biyu zai fi na farko inganci da samun ci-gaba.
Har ila yau, ya gargadi mambobin adawa da su guji yin fada da gwamna da mambobin jam’iyya mai mulki.
Yusuf, ya kuma yaba wa shugabannin addini da na kauyuka, bisa goyon baya da addu’o’i game da nasarar gwamnatin Aminu Tambuwal.
You must log in to post a comment.