Home Labaru Takaddama: Shugabannin Kudanci Da Tsakiyar Nijeriya Sun Ce Ba Su Kori Fulani...

Takaddama: Shugabannin Kudanci Da Tsakiyar Nijeriya Sun Ce Ba Su Kori Fulani Ba

452
0

Kungiyar shugabannin al’ummomin yankunan kudu da na arewa ta tsakiya, sun ce ko da wasa ba su taba cewa Fulani makiyaya su bar yankunan su kamar yadda Dattawan Arewa su ka basu umurnin komawa gida ba.

A cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, kungiyar ta bayyana damuwa a kan rahoton kiran da shugaban kungiyar dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi ya yi wa Fulanin cewa su koma yankin su.

shugaban kungiyar dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi

Sanarwar ta ce, shugabannin kudancin Nijeriyar da Arewa ta tsakiya ba su da matsala da Fulani makiyaya, saboda sun dade su na zama tare da su kuma su na gudanar da ayyukan su ba tare da tsangwama ba.

Kungiyar ta bukaci shugaba Buhari ya taka wa Farfesa Ango Abdullahi da mukarraban sa birki, a kan abin da su ka kira kalaman da ka iya haifar da yaki.