Home Labaru Rashin Tsaro: Shugabannin Majalisun Dokoki Na Tarayya Sun Gana Da Shugaba Buhari

Rashin Tsaro: Shugabannin Majalisun Dokoki Na Tarayya Sun Gana Da Shugaba Buhari

202
0

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya yi karin haske dangane da tattaunawar sirrin da shugabannin majalisa su ka yi da Shugaba Muhammadu Buhari game da lamarin tsaron Nijeriya.

Sanatan ya ce ya gana da shugaba Buhari tare da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila   a Fadar shi da ke Abuja.

Shugabannin Majalisun Dokoki sun gana da shugaba buhari

Ya ce dukkan su sun amince da cewa, akwai matukar bukatar yin Taron Kasa a Kan Matsalar tsaro, wanda ya ce bangaren gwamnati za su gudanar da na su taron, sannan bangaren majalisa su gudanar da na su daban.

Sanatan ya kara da cewa, sun tattauna a kan neman mafita, inda a karshe su ka amince da cewa, bangarorin biyu za su hada kai domin gudanar da taron na kasa a kan matsalar tsaro.

Ya ce hakan ya na da tasiri, saboda yayin da su ke bada gudummawa a bangaren sha’anin majalisa, bangaren gwamnati ke da alhakin gudanar da ayyukan da su ka bijiro da su a karkashin doka.