Home Labaru Kudiri: Majalisar Wakilai Ta Sahale Wa Buhari Daukar Mashawarta 15

Kudiri: Majalisar Wakilai Ta Sahale Wa Buhari Daukar Mashawarta 15

300
0

Majalisar wakilai ta amince wa shugaba Muhammdu Buhari ya dauki sabbin mutane 15 a matsayin masu ba shi shawara a kan al’amuran da su ka shafi sha’anin mulki kamar yadda ya bukata.

Shugaba Buhari dai ya aike wa majalisun dokoki na tarayya wasikar da ke kunshe da wannan bukata kamar yadda doka ta tanada, inda ya nemi amincewar su domin nada mashawarta.

Dan majalisa Garba Ado daga jihar kano ne ya gabatar da kudirin ga majalisar, da nufin ta amince da bukatar shugaban kasa yayin zaman suna ranar Alhamis.

Dan majalisa Garba Ado

Garba Ado ya ce, amincewa da bukatar shugaban kasa ta dace da sashe na 151 (1) na dokokin kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekara ta 1999.

Sai dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba majalisun damar kayyade adadin mashawartan da shugaban kasa ke so ya nada, da albashin su da kuma alawus-alawus. �9��}��?