Home Labaru Takaddama: Saraki Ya Koka Da Matakin EFCC Na Garkame Gidajen Shi A...

Takaddama: Saraki Ya Koka Da Matakin EFCC Na Garkame Gidajen Shi A Legas

340
0
Sanata Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa

Mai ba shugaban majalisar dattawa Sanata Sarakin shawara ta fuskar yada labarai, ya ce matakin da hukumar EFCC ta dauka ba wani abu ba ne illa bata sunan Sanatam kuma hakan ya saba dokar Nijeriya

Yanzu haka dai gidaje a kalla biyar mallakar Sanata Bukola Saraki na ci-gaba da zama a garkame, bayan hukumar EFCC ta rufe su a Lagos.

Hukumar EFCC dai ta zargi Bukola Saraki da mallakar gidajen a lokacin ya ke gwamnan jihar Kwara ba bisa ka’ida ba.

Sai dai Saraki ya musanta zargin, inda ya ce tuni aka wanke shi a baya, ya na mai bayyana matakin da cewa bi-ta-da-kulli kawai ake yi ma shi.A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara ta fuskar yada labarai Yusuph Olaniyonu ya fitar, ya ce matakin da hukumar EFCC ta dauka bata sunan Saraki ne kawai, ya na mai cewa hukumar EFCC ta dauki matakin ne domin cimma wani buri da ke da nasaba da siyasa kadai.

Leave a Reply