Home Labaru Ranar Dimokaradiyya: Ba Wani Gagarumin Bikin Sharholiya Za A Yi Ba –...

Ranar Dimokaradiyya: Ba Wani Gagarumin Bikin Sharholiya Za A Yi Ba – Lai Mohammed

497
0
Lai Mohammed, Ministan Labarai Da Al’adu

Bikin rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu da za a yi a ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2019 ba zai kasance wani gagarumin bikin sharholiya ba kamar yadda ministan labarai da al’adu Lai Mohammed bayyana.

Lai Mohammed, ya ce wasu bukukuwa da aka shirya yayin bikin rantsarwar za su gudana ne a ranar 12 ga watan Yuni na farko da za a yi a matsayin ranar damokradiyyar Nijeriya.

Ministan ya ce an yanke hukuncin yin bikin rantsarwar cikin sauki ne a wajen taron majalisar zartarwa da ya gudana a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu.

Ya ce, sai dai an tura wasikar gayyata ga dukkan shugabannin duniya domin su halarci bukukuwan da aka shirya na bikin ranar Damokradiya a ranar 12 ga watan Yuni.Lai Mohammed, ya ce Nijeriya ba za ta iya gudanar da manyan bukukuwa biyu cikin tazarar makonni biyu ba, sai dai ya ce za a sanar da cikakken bayanin bukukuwan da aka shirya a wajen taron labarai na duniya da aka shirya yi a ranar 20 ga watan Mayu a Abuja.

Leave a Reply