Home Labaru Nijeriya 2023: Ba Za A Samu Zaman Lafiya Ba Sai Igbo Ya...

Nijeriya 2023: Ba Za A Samu Zaman Lafiya Ba Sai Igbo Ya Zama Shugaban Kasa – Nwobodo

350
0
Sanata Jim Nwobodo, Tsohon Gwamnan Jihar Anambra

Tsohon gwamnan jihar Anambra Sanata Jim Nwobodo, ya ce Nijeriya ba za ta taba samun zaman lafiya ba har sai dan kabilar Igbo ya zama Shugaban kasa.

Nwobodo ya bayyana haka ne, yayin da ake gudanar da bikin cikar sa shekaru 79 a Enugu, ya bukaci al’ummomin Igbo su hada kai su mara wa duk wanda ya tsaya takara daga yankin kudu maso gabashin Nijeriya baya.

Tsohon gwamnan, ya kuma yi kira ga bangaren shari’a, su rika gudanar da ayyukan su a kan adalci, cewa ta bangaren shari’a ne kadai za su iya ceto Nijeriya daga durkushewa. A karhe ya jinjina wa gwamnan jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi, wanda ya ce ya hada kan ‘yan siyasar jihar cikin aminci da girmama juna.