Home Labaru Takaddama: Obono-Obla Ya Tafka Manyan Laifuffuka Guda 50 – Malami

Takaddama: Obono-Obla Ya Tafka Manyan Laifuffuka Guda 50 – Malami

348
0
Abubakar Malami, Ministan Shari’a
Abubakar Malami, Ministan Shari’a

Ministan shari’a Abubakar Malami, ya zargi tsohon shugaban kwamitin kwato dukiyoyin gwamnati da aka sace Okoi Obono-Obla da gudanar da wasu haramtattun bincike-bincike masu yawa yayin da ya ke ofis.

Malami ya bayyana haka ne, a cikin wani rahoto da ya aika wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, inda ya ce a hukumance bincike biyu kadai aka ba Obla damar gudanarwa, amma ya yi gaban kan sa ya gudanar da bincike-bincike har guda 50.

Idan dai ba a manta ba, a cikin watan Nuwamba ne gwamnatin shugaba Buhari ta tsige Obla daga mukamin sa, sannan ta nemi ya mika kan sa ga hukumar yaki da rashawa ICPC, amma bai aikata hakan ba.

Sai dai a nasa bangaren, Obla ya aika wa shugaba Buhari budaddiyar wasika, inda ya ce bita da kulli Osinbajo ke yi ma shi saboda ya na biyayya ga shugaba Buhari.

Leave a Reply