Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Gindaya Sharudan Bude Iyakokin Nijeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Gindaya Sharudan Bude Iyakokin Nijeriya

559
0

Gwamnatin tarayya ta gindaya sharudan da ta ce ya zama wajibi a bi idan har za ta sake bude iyakokin ta.

Ta ce ya zama dole kasashen ECOWAS su mutunta dokar asali, inda ta sha alwashin cewa Nijeriya ba za ta sake lamuntar sauya ainihin kayayyakin da aka shigo da su daga waje ba.

Gwamnatin tarayya ta cigaba da cewa, duk wasu kaya da za su shigo Nijeriya daga wata kasa ‘yan kungiyar ECOWAS dole ya kasance an sarrafa su daga kayan kasar, ko ya kasance ya kunshi kashi 30 cikin 100 na kayan cikin kasar. Ta jaddada cewa, idan har za a shigo da kayayyaki kasuwar Nijeriya daga wata kasa, ya zama dole kasar ta yi wa kayan rakiya kai tsaye har zuwa kan iyaka.