Home Labaru Kotun Daukaka Kara Ta Kori Dan Majalisar Alhassan Ado Doguwa

Kotun Daukaka Kara Ta Kori Dan Majalisar Alhassan Ado Doguwa

1232
0
Alhassan Ado Doguwa

Kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna, ta kori dan majalisa mai wakiltar mazabar Tudun Wada da Doguwa ta jihar Kano kuma shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa.

Ado Doguwa dais hi ne mutum mafi girman kujera na uku a majalisa bayan shugaban majalisa da mataimakin sa.

Kotun, ta yi watsi da zaben kananan hukumomi biyu da Ado Doguwa ke wakilta bisa zargin magudin da aka tafka a zaben watan Febrairu na shekara ta 2019.

Alkalan kotun, a karkashin jagorancin mai shari’a Oludotun Adefope-Okojie, sun yi ittifakin cewa ba zai yiwu a amince da sakamakon zaben ba, saboda babu sunayen wasu ‘yan takara a takardar sakamakon da hukumar zabe ta sanar.

Kotun, ta ce hukumar zabe ta tafka babban kuskuren rubuta sakamakon jam’iyyu biyu kadai daga cikin 53 da su ka yi takara.