Kungiyar kwadago ta Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan sake ba Chris Ngige, mukamin ministan kwadago karo na biyu.
Karanta Wannan: Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Bukatar Sa Almajirai A Tsarin Ilimin Boko
Shugaban kungiyar kwadago kwamared Ayuba Wabba, ya ce Ngige, bai cancanci ya jagoranci ma’aikatar ba idan har gwamnati ta na son yin aiki mai kyau da ma’aikata.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi ikirarin cewa ministocin sa sun taka rawar gani, kuma shi ne dalilin da ya sa, ya cigaba da tafiya da wasu daga cikin su.
Shugaba Buhari dai ya sake rantsar da sabbin ministocin sa 43, kuma cikinsu akwai 12 da ya fara aiki da su a wa’adi na farko kuma cikin su har da Chris Ngige.
An dai kai ruwa rana tsakanin Chris Ngige, da kuma kungiyar kwadago kan batun karin albashin na ma’aikata, kafin shugaba Buhari, ya amince da karin albashi mafi karanci na naira dubu 30 a watan Afrilu.
Shugaba Buhari ya
amince da matakin ne bayan kungiyar kwadago ta ba shugaban kasa wa’adi ya
amince da dokar ko ta tsunduma cikin yajin aiki wanda zai shafi kowane ma’aikaci.