Home Labaru Rashawa: Hukumar FRSC Ta Gargadi Jami’anta

Rashawa: Hukumar FRSC Ta Gargadi Jami’anta

281
0
FRSC
FRSC

Gamayyar jami’an hukumomin tsaro daban-daban a karkashin jagorancin hukumar yaki da rashawa da sauran laifuka makamanta haka, ICPC sun kama  jami’an hukumar kiyaye hadura 37 da laifin karban cin hanci da cin zarafin masu mota a manyan titunan Najeriya.

Kakakin hukumar kiyaye haddura Rasheedat Okoduwa, ta bayyana haka ga manema labarai, inda ta ce gamayyar ta kunshi jami’an hukumar ICPC da hukumar FRSC da kuma na hukumar SSS.

Rasheedat, ta ce tawagar sun kama sune a sakamakon rahoton da suka samu cewa wasu jami’an FRSC na karba kudi a hannun mutane a manyan tituna.

Ya ce hukumar ta gano cewa ayyukan cin zarafin jama’a ya yawaita a jihohin Kaduna, da Bauchi, da Abia, da Rivers, da Kogi da kuma Ogun, saboda haka zata dauki matakin  sallamar duk jami’in da aka kama ya na karban cin hanci daga hannun direbobi.