Home Labaru Takaddama: Naira Miliyan 300 Na Marayu Sun Yi Ɓatan Dabo A Asusun...

Takaddama: Naira Miliyan 300 Na Marayu Sun Yi Ɓatan Dabo A Asusun Kotun Musulunci

16
0

Hukumar kula da kotunan shari’ar muslunci ta jihar Kano, ta tabbatar da ɓatan wasu kudaden marayu sama da naira miliyan 300 da ke ajiye a asusun ɗaya daga cikin bankunan da ta ke ajiye kudaden ta.

Ta ce wani bincike da ta gudanar ya nuna cewa, an yi amfani da sa hannun bogi wajen fitar da kuɗaɗen daga asusun bankin kotun Shahuci, inda ta ajiye kudaden marayun da ake shari’ar rabon gadon su a gaban ta.

Babban akawun hukumar kula da kotun shari’ar musulunci ta jihar Kano Malam Abubakar Haruna Khalili ya shaida wa manema labarai cewa, kudaden da su ke zargin sun yi batan-dabo na marayu ne daban-daban da ake shari’ar su a gaban kotunan musulunci a sassan jihar Kano.

Ya ce an gano ɓatan kudaden ne a lokacin da aka je fitar da wasu kuɗaɗe da aka ajiye a asusun bankin, na wata shari’a tsakanin wani Ƙwara da wani mutum amma aka ce babu kudin a ciki.

Abubakar Haruna, ya ce abin ya rage bai wuce naira miliyan 9 ba, alhalin sun san su na da sama da miliyan naira Miliyan 100.