Home Labaru Kurungus: Femi Fani-Kayode Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC

Kurungus: Femi Fani-Kayode Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC

12
0

Tsohon ministan surufin jiragen sama Femi Fani-Kayode ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

An dai gabatar da Fani-Kayode a gaban shugaba Muhammadu
Buhari a fadar sa da ke Abuja, bisa jagorancin shugaban riko na
jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle na daga cikin
wadanda su ka karbi Fani-Kayode a jam’iyyar APC.

Femi Fani-Kayode, ya ce akwai dalilan da su ka tilasta ma shi
sauya sheka daga PDP zuwa APC, kuma daga ciki akwai neman
hadin kan kasa.