Home Labaru Wata Sabuwa: Wani Jirgin Yaki Ya Yi Barin Wuta A Yobe Ya...

Wata Sabuwa: Wani Jirgin Yaki Ya Yi Barin Wuta A Yobe Ya Kashe Fararen Hula Da Dama

24
0

Wani jirgin yaki da ba a tantance inda ya fito ba, ya yi ruwan wuta a yankin kauyen Buhari da ke karamar Yunusari ta jihar Yobe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama.

Al’ummar garin sun shaida wa manema labarai cewa, sun wayi gari ne da ganin jiragen yaki guda uku su na shawagi a sararin samaniyar garin.

Daga bisani daya daga cikin jiragen ya yi amon wuta a kan wani bangare na garin, kamar yadda wani da ‘yan’uwan sa su ka mutu a lamarin ya shaida wa manema labarai.

Ya ce da misalin karfe 8.30 na safe ne lamarin ya faru, inda daya daga cikin jiragen ya fada wani bangaren na garin ya na ta zubar da wuta, lamarin da ya sa duk gidajen da ke bangaren su ka lalace.

Shaidun ya cigaba da cewa, jirgin babba ne sosai irin na sojoji, amma ba su san ko na ina ne ba.