Home Labaru Takaddama: Jihar Yobe Ta Karbe Wani Filinta Daga Hannun Sojoji Kaduna

Takaddama: Jihar Yobe Ta Karbe Wani Filinta Daga Hannun Sojoji Kaduna

529
0
Mai Mala Buni, Gwamnar Jihar Yobe
Mai Mala Buni, Gwamnar Jihar Yobe

Gwamnatin jihar Yobe ta karbo daya daga cikin filin ta mai girman hekta 3 da rabi  daga hannun rundunar soji a Kaduna.

 Da yake mika filin ga wakilin gwamnatin jihar Yobe, kwamandan rundunar soji ta daya, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya bayyana cewa an warware badakalar batun filin ne sakamakon saka bakin da shugaban rundunar soji ta kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai ya yi.

Ya kara da cewa rundunar soji ta mika filin ga gwamnatin jihar ne saboda dalilan zaman lafiya da kuma girmama alakar da ke tsakanin su, kuma mika filin a hukumance zai ba gwamnatin jihar Yobe damar yin amfani da wurin domin gina duk abinda take so.

Da yake sa hannu akan takardun karbar filin a madadin gwamnatin Yobe, sakataren gwamnatin jihar, Baba Mallam Wali, ya ce an warware batun takaddama akan fili ne saboda kyakkyawar alaka da girmama juna dake tsakanin rundunar soji da gwamnatin jihar Yobe.

Ya ce gwamnatin jihar Yobe ta yi alkawari za ta yi amfani da filin wajen gina wani abu da zai taimaki mutanen jihar Yobe da ma kasa baki daya, kuma nan bada dade wa ba za a fara aikin kewaye filin.