Majalisar zartarwa ta tarayya fitar da kudi naira biliyan 166 domin yin kwaskwarima da kuma sabbin tituna 14 a Najeriya.
Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ne ya karanto takardar da ke dauke da bukatar aikin taron majalisar da ya gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ministan, ya ce ma’akatar ayyuka da gidaje ce ta shirya daftarin, da nufin samar da hanyoyin masu kyau domin samarwa matafiya musamman masu kasuwanci sauki daukan kaya daga wuri zuwa wuri.
Daga cikin titunan da aka lissafa aikin zai shafa sun hada da na Kontagora zuwa Rijau dake jihar Neja, inda za a gina har da gada guda biyu da Titin Kano zuwa Katsina, inda za a kara fadin titin daga shatale-talen Dawanau.
Sauran su hada da Titin Kontagora zuwa Bangi da titin Bonny Camp da kuma gadar Eko har zuwa gadar Apongbon ta jihar Legas, da Titin Irrua-Edenu zuwa Udomi-Uwessan wanda za a yi wa kwaskwarima a jihar Edo, da kuma Ilobu-Erinle a tsakanin Kwara da Osun, da kuma gadar Wudil wadda take sadarwa zuwa Gaban Komi kan By-pass a hanyar Maiduguri a jihar Kano.