Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC reshen jihar Sokoto, ta kama wasu manyan jami’an gwamnatin jihar Sokoto wadanda suka hada da ta kama Abdullahi Sa’idu, Darakta Janar na hukumar tsaro da Bashar Dodo-Iya, akawun hukumar kan zargin karkatar da naira miliyan 10 da ya kamata a biya albashin ma’aikata.
An kama masu laifin su biyu wadanda suka kasance mambobin kwamitin biyan jami’an tsaron a Sokoto, biyo bayan wata kara ta hadin gwiwa dauke da sa hannun jami’an hukumar 39 zuwa ga hukumar, kan zargin cewa an rike masu albashin watanni uku ba tare da kowani dalili ba.
Ma’aikatan sun ci gaba da zargin cewa masu laifin sun ki biyansu albashi, sannan sun karkatar da kudin zuwa ga amfanin kansu., kuma binciken farko ya tabbatar da zargin cewa masu laifin sun karkatar da kudin.

A yanzun hukumar na ci gab da gudanar bincike kan wadanda ake zargi kuma da za ran ta kammala za ta mika su ga kotu domin daukan mataki na gaba.