Home Labaru Takaddama: Jam’iyyar APC Ta Daukaka A Kan Hukuncin Zaben Gwamnan Bauchi

Takaddama: Jam’iyyar APC Ta Daukaka A Kan Hukuncin Zaben Gwamnan Bauchi

419
0
Uba Nana, Shugaban Jam’iyyar APC Jihar Bauchi
Uba Nana, Shugaban Jam’iyyar APC Jihar Bauchi

Jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi, ta daukaka kara a kan hukuncin da Kotun Daukaka Kararrakin Zaben Gwamna ta yanke.

Da ya ke jawabi a wajen taron manema labarai a Bauchi, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Uba Nana, ya ce ya zama wajibi su daukaka kara zuwa gaba, domin ba su gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba.

Ya ce ya na da yakinin da kuma fatan samun adalci a kotun gaba, tare da yin kira ga daukacin ‘yan jam’iyyar APC na jihar Bauchi cewa kada hukuncin da kotu ta yanke ya sare masu gwiwa.

Idan dai ba a manta ba, Kotun ta kori karar da jam’iyyar APC da dan takarar ta su ka shigar, domin neman a soke zaben da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya yi nasara.