Home Labaru Ilimi Karin Harajin: Mun Yi Ne Don Inganta Fannonin Lafiya Da Ilmi Da...

Karin Harajin: Mun Yi Ne Don Inganta Fannonin Lafiya Da Ilmi Da Ayyukan Ci Gaba – Buhari

811
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce an yi karin Harajin kayayyaki na VAT, daga kashi 5 cikin 100 kashi 7 da rabi domin a yi wa jama’a ayyukan inganta kiwon lafiya da ilmi da ayyukan raya kasa.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya ke gabatar da Kasafin shekara ta 2020 a zauren majalisar dokoki ta tarayya.

Idan dai ba a manta ba, a baya an ce an yi karin harajin ne domin a samu kudaden da za a rika biyan karin mafi kankancin albashin ma’aikata, sai dai yayin gabatar da kasafin, shugaba Buhari ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen inganta fannin kiwon lafiya da ilmi da ayyukan raya al’umma.

Ya ce Karin kudaden harajin, jihohi da kananan hukumomi ne za a rika ba kashi 85 cikin 100, domin su rika gudanar da ayyukan raya al’umma, wadanda ke yi masu wahalar aiwatarwa saboda karancin kudade. Sai dai gwamnati ta lissafa kayayyakin abinci, wadanda akasari talaka ke amfani da su a matsayin wadanda ba za a karbi harajin VAT daga gare su ba.