Home Labaru Takaddama: Iran Ta Sha Alwashin Daukar Fansar Kisan Qassem Soleimani Kan Trump

Takaddama: Iran Ta Sha Alwashin Daukar Fansar Kisan Qassem Soleimani Kan Trump

158
0

Shugaba Ebrahim Raisi na Iran ya sha alwashin daukar fansa kan tsohon shugaban Amurka Donald Trump game da kisan babban kwamandan askawaran sojin juyin juya halin kasar Qassem Soleimani a shekarar 2020.

Kalaman Ebrahim Raisi da ke zuwa lokacin da ake addu’o’in cika shekaru 2 na kisan da Amurka ta yiwa babban kwamandan akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman birnin Bagdad ranar 3 ga watan Janairun shekarar ta 2020, ya ce daukar fansa kan kisan Soleimani ya zama wajibi agare su.
Ba kadai a Iran ba, dukkanin kawayen kasar da ke yankin gabas ta tsakiya sun gudanar da jimamin na cika shekaru biyu da kisan na Qassem Soleiman tare da takwaransa na Iraqi wanda ya gudana bisa umarnin Donald Trump shugaban Amurka na wancan lokaci.
A cewar shugaba Ebrahim Raisi matukar ba a yiwa Donald Trump hukunci kan kisan gillar da ya yiwa kwamandojin da direbobinsu da masu tsaron lafiyarsu ba, ko shakka babu za su dauki fansa da kansu.

Leave a Reply