Home Labaru Bola Tinubu Ya Faɗa Wa Shugaba Buhari Kudirinsa Na Takara A 2023

Bola Tinubu Ya Faɗa Wa Shugaba Buhari Kudirinsa Na Takara A 2023

207
0

Jigon jam’iyyar APC  Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya sanar da shugaba Muhammadu Buhari kudirin sa na neman takarar shugaban ƙasa a zaben shekara ta 2023.

Bola Ahmed Tinubu ya bayyana haka ne, yayin da ya ke zantawa manema labarai, jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja.

Ya ce ya sanar da shugaba Muhammadu Buhari kudirin sa, amma bai shaida wa ‘yan Nijeriya ba, ya na mai cewa har yanzu ya na shawari ne.

Duk da tun baya akwai alamun ya na sha’awar kujerar shugabancin Nijeriya,  Bola Tinubu ya kauce wa yin kalaman da za su nuna kudirin sa na tsayawa takara kai tsaye.  

Leave a Reply