Home Home Kasar Guinee: Jam’iyyun Siyasa Za Su Tunkarar Gwamnatin Soji

Kasar Guinee: Jam’iyyun Siyasa Za Su Tunkarar Gwamnatin Soji

241
0

A Kasar Guinea jam’iyyun siyasa 128 sun sanar da aniyar su ta tunkarar gwamnatin mulkin sojin kasar don matsa masu su fito da jadawalin mika Mulki hannun farar hula ba tare da jinkiri ba.

Matakin da yan siyasar kasar suka dauka na zuwa ne kusan kwannaki hudu da Amurka ta sanar da cire kasar ta Guinee daga cikin kasashen kungiyar ta AGOA masu huldar kasuwanci da Amurka.
A farkon watan janairun shekarar 2022, majalisar soji mai rike da mulkin kasar ta baiwa tsohon shugaban kasar Alpha Conde damar ficewa har idan ya na bukata.
Mai Magana da yawun jam’iyyun siyasan Cellou Dalein Diallo ya shaidawa taron manema labarai daukan wannan mataki a Conakry.
Tuni dai shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS suka nemi sojan na Guinea da su ga lallai an yi zabe cikin watanni 6.

Leave a Reply