Home Labaru Rikicin Zamfara: Majalisar Sarakuna Ta Bukaci Bincike Mai Zurfi A Kan ‘Yan...

Rikicin Zamfara: Majalisar Sarakuna Ta Bukaci Bincike Mai Zurfi A Kan ‘Yan Bindiga

393
0

Majalisar koli ta Sarakunan jihar Zamfara, ta bukaci gwamnatin tarayya ta kafa tawagar musamman domin gudanar da bincike a kan hare-haren ‘yan bindiga a jihar, domin zakulo wadanda ke da hannu da kuma tabbatar da cewa an hukunta su.

Shugaban majalisar Sarakunan kuma Sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad ya gabatar da bukatar a fadar sa, yayin da ministan harkokin cikin gida AbdulRahman Dambazau ya kai ziyara.

Sarkin, ya kuma bukaci gwamnati ta dauki matakin katse layukan sadarwa a jihar Zamfara, musamman a yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga zuwa wani lokaci, matakin da ya ce zai taimaka wajen dakile kokarin da wasu bata-gari ke yi wajen sanar da mahara shirye-shiryen da jami’an tsaro ke yi na murkushe su.

Sarkin ya kuma bukaci a tsaurara matakan tsaro a dukkan hanyoyin da mahara ke bi wajen kai wa jama’a farmaki.Janar Dambazau dai ya ziyarci jihar ta Zamfara ne bisa umarnin shugaba Muhammadu Buhari, kwanaki kadan bayan ‘yan bindiga sun tilasta wa jama’ar karamar hukumar Shinkafi kwana cikin daji sakamakon farmakin da su ka kai masu.

Leave a Reply