Home Labaru Takaddama: Gwamnatin Imo Ta Ba ‘Yan Sanda Umurnin Kama Rochas Okorocha

Takaddama: Gwamnatin Imo Ta Ba ‘Yan Sanda Umurnin Kama Rochas Okorocha

219
0

Gwamnatin jihar Imo, ta bada umurnin kama tsohon gwamnan jihar sanata Rochas Okorocha bisa laifi cin zarafin wani jami’in gwamnati Mista Jasper Ndubuaku.

Uche Onyeaguocha, Sakataren gwamnatin jihar Imo

Sakataren gwamnatin jihar Uche Onyeaguocha, ya bada umurnin ne bayan shugaban kwamitin kwato dukiyoyin gwamnati Jasper Ndubuaku ya kai karar cewa an yi masa duka a gidan Okorocha.

Ya ce gwamnatin jihar za ta sa ido a kan Rochas Okorocha,tare da yin kira ga jama’ar jihar su kamashi a duk inda suka ganshi.

Kamfanin dillacin labarai na Nijeriya, ya bada rahoton wani faifan bidiyo da ya bayyana a yanar gizo, inda aka ga wasu ‘yan daba suna dukan Jasper Ndubuaku a gidan Okorocha dake Spibatt a birnin Owerri.

Gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewa, Okorocha ya dauki nauyin ‘yan daba domin dukan Ndubuaku, wanda mai ba gwamnan jihar shawara ne na musamman a kan harkokin tsaro.

Lamarin daiya biyo bayan gargadin da sarakunan jihar suka yiwa Rochas a kan kokarin kawowa kwamitin bincike mishkila, yayin da Kwamishanan ‘yan sanda na jihar ya ce za su gudanar da bincike a kan lamarin. ��“r�