Home Labaru Kisan Rabaren: IGP Ya Yi Umurnin Tsaurara Matakan Tsaro A Cibiyoyin Bauta

Kisan Rabaren: IGP Ya Yi Umurnin Tsaurara Matakan Tsaro A Cibiyoyin Bauta

258
0

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya nuna matukar damuwa akan hare-haren baya-bayan nan da ake kaddamarwa akan malaman addini a wasu yankunan kasar nan.

Mohammed Adamu ya umurci kwamishinonin ‘yan sanda na dukkan jihohin Nijeriya, cewa daga yanzu su maida hankali akan malamai sannan su kara tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin bauta a fadin Nijeriya.

Frank-Mba-PRO

A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya DCP Frank Mba ya fitar, ya ce shugaban ‘yan sandan ya umurci kwamishinan ‘yan sanda na jihar Taraba ya zakulo makasan Reveran Father David Tanko, wanda a cewarsa, wasu da ba a san ko su wanene ba sun kashe shi a a kauyen Kpankufu da ke hanyar Wukari a hanyarsa ta zuwa kauyen Kofai Ahmadu a jihar Taraba.

Yace Shugaban ‘yan sandan, ya kuma umurci Mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya mai kula da sashen bincike na rundunar da za samar da karin kayayyakin bincike domin taimakawa wajen binciken lamarin.