Home Labaru Siyasar Kano: Kotu Ta Kori Dambazau A Matsayin Dan Majalisa Ta Ba...

Siyasar Kano: Kotu Ta Kori Dambazau A Matsayin Dan Majalisa Ta Ba Dan Takarar PDP

736
0

Rahotanni na cewa, Kotun sauraren koraf-korafen zabe ta jihar Kano, ta soke zaben Shamsuddeen Dambazaua matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Sumaila da Takai.

Kotun daita umurci hukumar zabe ta bada takardar shaidar cin zabe ga Surajo Kanawa na jam’iyyar PDP.

Shamsuddeen,wanda bai yi takarar zabe ba, amma ya zo na biyu a zaben fidda gwanin jam’iyyar APC, a lokacin da babbar kotun tarayya da ke Kano ta watsar da tsohon hadimin Shugaban kasa Kawu Sumaila, bayan wata kara da aka shigar kafin zabe.

Idan dai za a iya tunawa, Shamsuddeen yayi karar hukumar zabe daAPC da Kawu Sumaila, inda ya kalubalanci tsayar da Sumaila a matsayin dan takarar jam’iyyar APC.