Home Labaru Takaddama: Dokar Kirkiro Sabbin Masarautu Ta Tsallake Karatun Farko A Kano

Takaddama: Dokar Kirkiro Sabbin Masarautu Ta Tsallake Karatun Farko A Kano

255
0

Kudurin dokar kirkirar sabbin masarautu ya tsallake karatu na farko a majalisar dokoki ta jihar kano.

Majalisar dai ta soma zaman nazari ne a kan takardar da aka shigar a gaban ta ta neman kirkirar sabbin masarautu hudu a fadin jihar.

Rahotanni sun ce, majalisar ta na kokarin yi wa dokar masarautar ta shekara ta 1984 kwaskwarima ne, bayan bukatar da ta ce wasu kungiyoyi sun shigar gaban ta a kan neman sake kirkirar masarautu a Jihar.

Sai dai tun kafin a fara zaman majalisar, mutanen kananan hukumomin garuruwan da za a daga hakiman su, sun yi wa majalisar dafifi da zummar nuna goyon bayan su ga majalisar bisa yunkurin da ta ke yi.