Home Labaru Kudin Makamai: Begore Ya Ce Ya Ba Kwamishinan ‘Yan Sanda Naira Miliyan...

Kudin Makamai: Begore Ya Ce Ya Ba Kwamishinan ‘Yan Sanda Naira Miliyan 10

258
0

Babban Lauya Mohammed Dele Belgore da ke fuskantar zargin karkatar da naira miliyan 450 gabannin zaben shekara ta 2015, ya sanar da wata babbar kotu da ke Legas cewa daga cikin kudaden ya ba kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kwara a wannan lokacin naira miliyan 10.

Hukumar EFFCC ta gufanar da shi a gaban babbar kotun da ke Legas bisa zargin amfana da naira miliyan 450 daga cikin dala miliyan 115 da tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Madueke ta fitar a zaben shekara ta 2015.

EFCC, ta ce an gayyaci Belgore tare da tsohon ministan tsare-tsare Farfesa Abubakar Suleimen a reshen wani banki da ke Illorin a ranar 26 ga watan Maris na shekara ta 2015, domin sa hannu da kuma karbar kudi naira miliyan 450.

Belgore, ya kuma gaskata gayyatar da manajan bankin ya yi masa a ranar 26 ga watan Maris na shekara ta 2015, domin karbar naira miliyan 450, ya ce amma ya karkare da barin bankin ba tare da kudaden ba.

Leave a Reply