Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi, ya ce matsalar tsaro a arewacin Nijeriya ta fi muni a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari fiye da zamanin mulkin Jonathan.
Farfesa Ango Abdullahi, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ba ya tabuka abin kirki wajen magance matsalar.
Ango Abdullahi dai ya na maida martani ne, game da tsokacin da mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya yi, inda ya ce kasancewar shugaba Buhari ya fito daga Daura, hakan ba ya nufin ba za a iya aikata mummunan laifi a garin ba ko kuma a ba shi fifiko na musamman.
Idan dai a a iya tunawa, a watan da ya gabata, Kungiyar Dattawan Arewa ta ce, za a cigaba da fama da hare-haren ‘yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto, muddin ba a tanadi yanayin aiki mai kyau ga jami’an ‘yan sanda ba.