Home Labaru Takaddama: Bindow Da Makarraban Sa Na Yin Watandar Kadarorin Jihar Adamawa –...

Takaddama: Bindow Da Makarraban Sa Na Yin Watandar Kadarorin Jihar Adamawa – Fintiri

622
0
Ahmadu Fintiri, Zababben Gwamnan Jihar Adamawa

Zababben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya koka kan yadda gwamna mai barin gado Jibirilla Bindow da makarraba sa ke Watanda da dukiyar jihar.

Shugaban kwamitin John Yahaya shirya mika mulki John Yahaya ya bayyana haka a lokacin da yake kokawa kan halin da jihar ke ciki,  ya ce gwamnatin jihar ta rika bada kwangiloli masu yawa sannan ta na biya tun ba a yi aikin.

Yahaya ya ce gwamnatin na raba wa makarrabanta wasu daga cikin kadarorin jihar ba tare da an bi doka ba, sannan kuma tuni gwamna Bindow ya biya kansa kudin sallama bayan ga dubban ma’aikatan jihar da ba iya biyan su albashi ba.

Ya kara da cewar tun kafin a shirya yadda za a biya sabon tsarin albashi, gwamna Umar Bindow ya bayyana cewa jihar za ta biya sannan kuma yana ta daukan sabbin ma’aikatan da bai dauke su ba a baya.Sai dai mai Magana da  yawun  gwamnatin jihar, Ahmed Sajoh, ya karyata zargi , inda ya ce kada kwadayin mulki ya rude su, saboda  har yanzu Bindow ne gwamnan jihar Adamawa, ko kuwa don zai ta fi shi ke nan sai a daina aiki a jihar.

Leave a Reply