Shugabar kotun daukaka kararrakin zaben shugaban kasa, Zainab Bulkachuwa ta yi barazanar cewa za ta yi maganin lauyoyi masu kai korafe-korafe ga ’yan jarida da kuma yin sharhi akan karar da ke a gaban kotun.
Bulkachuwa, ta ce duk lauyan da aka kama ya na sharhin kararrakin a kafafen yada labarai bayan zaman kotu, to kotun daukaka kara za ta yi maganin sa.
Zainab mai shari’a ta bayyana hakan ne a lokacin da take gargadin a wurin kaddamar da fara zaman kotun a Abuja, ta ce irin wadannan rubuce-rubucen da sharhin na kawo wa kotu cikas da kuma tarnaki ga yanke hukunci tare da jefa waswasi ga jama’a a kan hukuncin da kotu za ta yanke.
Bulkachuwa, ta kara da cewar wasu na rubuce-rubuce a shafin yanar gizo ko surutai a gidajen radiyo da talbijin su na yanke hukuncin mai laifi da mai gaskiya a wasu shari’o’in da ke gaban kotu da ba a rigaya aka yanke musu hukunci ba. Daga karshe shugabar kotun daukaka kararrakin zaben ta ce wannan gargadi bai tsallake kan jam’iyyun siyasa da magoya bayan su ba.
You must log in to post a comment.