Kungiyar Boko Haram sun kai hari a Maiduguri na jihar Borno, inda suka kashe mutane biyar suka jikkata wasu da dama.
Wani mazaunin garin mai suna Sunday Solomon ya ce ‘yan ta’addan sun kawo farmaki gidansa da ke Njimtilo a Maiduguri inda suke kashe mutane kuma suka yi awon gaba da kayayyakin abinci da wasu abubuwa masu muhimmanci.
Solomon, wanda ya sha da kyar bayan harsashi ta shafi shi ya ce Allah ne ya kiyaye shi kuma shi da iyalansa suka buya yayin da suka ji harbe-harben bindiga da ‘yan ta’addan ke yi.
Ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun yi tafiyarsu bayan aikata mummunan barna tare da sace wayoyin salula da kayan abinci.
Wani shaidan ganin ido Pete Ogeleh wanda aka kai masa hari a gidansa ya ce ‘yan ta’addan sun yi awon gaba da wani Isaac Dibal da wasu mutanen hudu a ma’aikatan kamfanin sadarwa na Airtel. Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Borno Bello Danbatta, ya ce gawar mutane hudun da suka rasu suna dakin ajiye gawa na wani asibitin kwararru na jihar.
You must log in to post a comment.