Home Labaru Ta’addanci: An Kashe Sojoji 8 A Monguno Dake Jihar Borno

Ta’addanci: An Kashe Sojoji 8 A Monguno Dake Jihar Borno

1278
0

Rahotanni na cewa dakarun sojin Najeriya takwas ne aka kashe wasu da dama suka bazama cikin daji sakamakon wani harin  kwantan-bauna da wasu da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai  a kan titin Monguno zuwa Maiduguri na jihar Borno.

Wani mazaunin garin Marte ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC sun ga  motoci uku kirar TATA cike da sojoji a kusa da wani kauye da ake kira Gasarwa, inda suka fito daga garin Munguno a yayin da suke kan hayar su ta shiga Mungonan.

Ya kara da cewa shigarsu garin Munguno ba jimawa suka  ga motoci na shigar da gawar sojoji cikin barikin soji na Mai Malari da ke garin na Munguno.

Rahotanni sun ce baya ga kisan sojojin, maharan sun yi awon gaba da makamai masu yawa.

Sai dai rahton yace kokarin jin ta bakin sojoji abun ya ci tura  kuma kawo yanzu, babu wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar game da al’amarin.

Hari dai na zuwa ne kasa da makonni biyu da kungiyar Boko Haram ta kai wasu hare-hare a garuruwan Konduga da Gubio da Magumeri na jihar Borno.