Mahukunta a hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, sun ce ba su da masaniya a kan labarin da ke yawo dangane da garkame wasu gidajen Sanata Bukola Saraki a Legas.
Idan dai za a iya tunawa, wasu rahotanni sun ce Hukumar EFCC ta kwace wasu gidaje mallakar shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki.
Mukaddashin shugaban sashen yada labarai da sanarwa na hukumar EFCC Tony Orilade, ya shaida wa manema labarai cewa ba shi da masaniya a kan lamarin.
Tuni Bukola Saraki ya zargi hukumar EFCC da yi masa bi-ta-da kulli domin daukar fansa irin ta siyasa a madadin iyayen gidan su da ke gwamnati.
A lokacin da hukumar EFCC ta gurfanar da shi a shekara ta 2016 a gaban kotun da’ar ma’aikata, EFCC ta shaida wa kotun cewa Saraki ya mallaki wasu gidaje a kan titin Macdonald da ke unguwar Ikoyi a Legas, amma ta yi zargin bai bada cikakken adireshin su ba.