Home Labaru Kuncin Rayuwa: Shugaba Buhari Ya Ce Ya Na Matukar Tausayin Talakawan Nijeriya

Kuncin Rayuwa: Shugaba Buhari Ya Ce Ya Na Matukar Tausayin Talakawan Nijeriya

423
0
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa bisa mummunan halin da talakawa da almajirai ke ciki, inda ya kalubalanci masu ruwa da tsaki su gaggauta daukar matakan magance matsalar.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin bude bakin azumi tare da mataimakin sa Yemi Osinbajo da Ministoci da Hafsoshin tsaro da wasu shugabannin hukumomi da cibiyoyin gwamnati a fadar sa da ke Abuja.

Ya ce a duk lokacin da ya ke zagaya sassan kasar nan, babban abin da ke damun sa shi ne halin da talakawa ke ciki a Nijeriya, inda za a rika ganin matasa da almajirai da yagaggun tufafi da robobin bara a hannun su, su na neman abin da za su ci.

Shugaba Buhari, ya ce neman ilimi ga wadannan mutane ya na da matukar wahala, yayin da ya ce masu ruwa da tsaki sun gaza, domin kuwa akwai bukatar samar da wani shirin bada ilimi ga mutanen da ke fama da matsanancin talauci.