Home Labaru Takaddama: An Maka Buhari Kotu Saboda Rashin Sallamar Shugabannin Tsaro

Takaddama: An Maka Buhari Kotu Saboda Rashin Sallamar Shugabannin Tsaro

228
0

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bukaci shugaba
Muhammadu Buhari ya cire duk shugabannin tsaro sakamakon
gaza samar da tsaro bisa karar sa da aka kai kotun.

Korafin da dan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam’iyyar
AAC, Alhaji Sa’id Uba ya yi, ya nemi shugaba Buhari ya yi
gaugawar daukar mataki, domin ya gaza kulawa da dukiyoyi da
rayukan ‘yan Nijeriya.

Sauran wadanda ake karar sun hada da Antoni janar na kasa, da
majalisar tarayya, da shugaban majalisar dattawa, da shugaban
rundunar sojin kasa da shugaban sojojin ruwa da na sama da
kuma shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya.

Sa’id Uba, wanda ya shigar da karar a madadin wadanda
matsalar rashin tsaro ta shafa a arewacin Nijeriya, ya kuma
bukaci shugaba Buhari ya biya wadanda lamarin ya shafa diyyar
Naira Biliyan 100, sannan ya bukaci kotu ta tilasta Buhari ya
sauke shugabannin tsaro saboda rashin ba Nijeriya tsaro.

Haka kuma, ya bukaci su yi gaugawar rubuta wasikar bada
hakuri ga ‘yan Nijeriya a cikin kwanaki bakwai, inda ya
bayyana yadda mutane da dama su ka rasa gidaje da iyalai da
dukiyoyin da su ka mallaka sanadiyyar rashin tsaro.