Home Labaru Boko Haram: Zulum Ya Gana Da Shugaba Deby A Kan ‘Yan Gudun...

Boko Haram: Zulum Ya Gana Da Shugaba Deby A Kan ‘Yan Gudun Hijirar Borno A Chadi

203
0

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, da Jakadan
Nijeriya a kasar Chadi Zannah Umar Bukar Kolo, sun hadu da
shugaban kasar Chadi Idriss Deby da Jakadan shi na Nijeriya
Abakar Saleh Chahaimi, domin tattaunawa a kan hanyoyin
maido ‘yan gudun hijirar Nijeriya da ke kasar.

Da yawa daga cikin ‘yan gudun hijirar dai sun tsere ne daga
jihar Borno zuwa Chadi tun a shekara ta 2014, sakamakon hare-
haren Boko Haram.

Mai ba gwamna Zulum shawara a kan harkar yada labarai
Malam Isa Gusau, ya ce sun yi taron ne domin bin hanyar da za
a maido ‘yan gudun hijirar zuwa Nijeriya.

A wajen taron, Gwamna Zulum ya ce gwamnatin Chadi ta na
kulawa da ‘yan gudun hijirar, don haka ya je ne ya mika sakon
godiya shugaban kasar a kan karamcin da ake yi wa ‘yan
Nijeriya a kasar Chadi.