Home Labaru Gargadi: Kada Ku Yarda A Dirka Maku Rigakafin Korona — Dino Melaye

Gargadi: Kada Ku Yarda A Dirka Maku Rigakafin Korona — Dino Melaye

228
0

Tsohon dan majalisar Dattawa Sanata Dino Melaye, ya gargadi
‘yan Nijeriya da gwamnatin tarayya cewa kada su kuskura su
biye wa Turawa su karbi maganin riga-kafin cutarKorona su
dirka wa mutane.

Dino Melaye ya ce maganin ba gaskiya ba ne, domin ya ce zuwa
yanzu wadanda aka yi wa allurer a wasu kasashen waje duk sun
mutu cikin kwanaki uku.

Ya ce ya na kira ga mahukuntan Nijeriya da na kasashen Afrika,
cewa kada su yarda a shigo da wannan magani domin ba gaskiya
ba ne, kawai ana so ne a yi gwajin shi a jikin bakaken fata su yi
ta mutuwa.

Sanatan ya kara da cewa, an sha fama da cututtukan Kansa da
Kanjamau da Ciwon Siga kuma sun yi ta kashe mutane sama da
tsawon shekaru 40, amma ba a taba samu riga-kafin sa ba sai
yanzu a ce wai an samo maganin a lokaci guda.

Leave a Reply