Jami’an hukumar kula da muhalli a birnin Lagos, sun kai samame gidan wani mutum da ya ajiye zaki a matsayin maigadin sa.
Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, jami’an sun je gidan ne a ranar Juma’ar da ta gabata, bayan mazauna unguwar sun kai korafin makwabcin su ya ajiye Zaki a gidan sa, wanda dan asalin kasar Indiya ne da ya ke zaman haya.
Bayan an dauke zakin zuwa gidan adana namun daji na jihar, jami’an tsaro sun kama mutumin domin tuhumar sa a kan dalilin da ya sa zai ajiye dabba mai hadari a wurin zaman jama’a da ke unguwar Victoria Island.
Rahotanni
sun ce mutumin ya yi wa mai gidan karya ne, cewa zai zauna zaman haya ne ba
tare da ya shaida ma shi cewa zai ajiye zaki ba.
You must log in to post a comment.